KennywoodMatan arewa

Yadda saurayina ya lakada min mummunan duka bayan shekarun da muka kwashe muna zaman dadiro, cewar Muneerat Abdussalam

Yadda saurayina ya lakada min mummunan duka bayan shekarun da muka kwashe muna zaman dadiro, cewar Muneerat Abdussalam

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

Yadda saurayina ya lakada min mummunan duka bayan shekarun da muka kwashe muna zaman dadiro, cewar Muneerat Abdussalam

A wani bidiyo wanda Muneerat
Abdussalam fitacciyar mai sayar da magungunan mata da maza a kafafen sada zumuntar zamani ta saki cike da hawaye, tayi karin bayani.

Dama tun safiyar Litinin ta bayyana yadda bariki tayi mata atishawar tsaki inda, yanzu haka ta rasa makama kasancewar ko kudin magani ta rasa.

A bidiyon wanda aka ga yadda saurayinta ya molar mata da fuska sabida tsabar dukan da yayi mata, ta bayyana yadda ta kai kara caji ofis amma ‘yan sanda suka mayar da maganarta shirme.

Tace, ta kwashe lokaci mai tsawo suna zama da matashin wanda yayi alkawarin auren ta, ashe dan daba ne kuma cikakken dan ta’adda ne bata sani ba.

Ta shaida yadda yake zuwa dakinta da tsakar dare tare da balle mata kofa sannan ya tumurmusata da zarar tayi masa kankanin abu wanda ya hassala shi.

Ta kara da cewa, ya tsere mata da kayan data aike shi ya sanya mata a mota masu kimar dubu dari uku da ‘yan kai.

Ta cigaba da shaida cewa, har guduwa tayi daga garin da suke don ta tsira daga sharrinsa bayan samun labarin ta’addancinsa.

A cewarta, tana neman taimakon jama’a kuma tayi nadamar gaba daya abubuwan da ta aikata a rayuwarta na bariki da biye-biyen maza.

Ta bayyana yadda take rayuwa cike da tashin hankali sannan saurayin nata yana bata hakuri idan sun yi fada daga bisani kuma yayi mata abinda ya zarce na baya.

Allah karabamu da aikin dana sani ameeeen Suma ameeen zamuso mukarbi rayinku a shashenmu na tsokaci akan wannan batuna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button