Yadda Matashi Ya Rasa Ransa Yana Cikin Gwada Kwazonsa Akan Wata Budurwa A Dakin Otal
Yadda Matashi Ya Rasa Ransa Yana Cikin Gwada Kwazonsa Akan Wata Budurwa A Dakin Otal

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW
Yadda Matashi Ya Rasa Ransa Yana Cikin Gwada Kwazonsa Akan Wata Budurwa A Dakin Otal
An tattaro bayanai akan yada Lanre, mamacin ya zage damtse yana ta lalata da matar a wani otal da ke garin Ondo ranar Laraba da yamma.
Har yanzu ba a bayyana suna ko kuma wani bayani dangane da matar ba. Wata majiya ta bayyana cewa:
“Matar ta sanar da jama’a ne bayan gane cewa mutumin ya rasu bayan ya kammala wanka daga gama lalatarsu da misalin karfe 9 na daren Laraba.
“Ihunta ne ya ja hankalin manajan otal din wanda daga bisani ya gayyaci ‘yan sanda daga ofishinsu da ke Enu-Owa don bincike.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mrs Funmilayo Odunlami ta ce mutuwar tasa ba ta lafiya lau bace, yayin da aka tuntubeta don jin bayani.
Amma a cewarta, yanzu haka ‘yan sanda sun shiga lamarin dumu-dumu don gano asalin silar mutuwarsa.
An tattaro bayanai akan yadda aka dauki gawar mamacin, inda aka kai ta ma’adanar gawa da ke jami’ar Kimiyya da ke Ondo.
A Wani Labarin Kuma
Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo a kudu maso yammacin Najeriya ta kama wani mutum mai shekara 54 da haihuwa bisa zargin ƙona agololinsa biyar a unguwar Fagun da ke garin Akure.
Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya yi hakan ne saboda matarsa wadda ita ce mahaifiyar waɗannan yara, ta ɓata masa rai saboda ta ƙi ba shi haɗin kai.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce yaro ɗaya ya rasu amma sauran huɗun suna karbar magani a cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Owo.
Ta ce tuni aka kama mutumin mai shekara 54 da haihuwa bisa zargin ƙona ‘ya’yan matar tasa biyar
Tace “Wani mutum ne ya zo ya bayar da rahoton abin da ya faru cewa wanda ake zargi Joseph, ya samu rashin fahimta tsakaninsa da matarsa, to saboda ya nuna rashin jin daɗin abin da ya faru – sai ya shiga ɗakin da yaran suke barci shi ne ya banka musu wuta.
Ta ƙara da cewa wannan wani lamari ne da ake zargin mutumin da yunƙurin kisan kai, kuma suna bukatar su yi bincike mai zurfi kan wanda ake zargin don sanin musabbabin faruwar abin da aka zargin cewa ya aikata.
Rundunar ‘yan sandan ta ce a halin da ake ciki, an tura wannan lamari zuwa ga sashen binciken manyan laifuka na (CID) don gudanar da binciken kwakwaf.
Kamar yadda ganau suka ce, tun farko rashin fahimtar ta yi tsanani bayan da uwar yaran ta ɓata wa mai gidanta rai saboda rashin fahimta da ta taso a tsakaninsu.
Sai dai wani ganau da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce wanda ake zargin ya yi yunƙurin kusantar matarsa to amma ta ƙi amincewa da bukatarsa- wani abu da ake zaton ya ɓata masa rai kuma ya nemi huce fushinsa kan yaran da ke barci, da ba su san hawa ba su san sauka ba.
Ana zargin Joseph da zazzage man fetur a cikin dakin da yaran ke barci, inda kuma nan take ya bankawa dakin wuta kuma ta gobara ta tashi.
Rundunar ‘yan sanda ta ce yaron wanda uban riƙon nasa ya yi ajalinsa ya ƙone ta yadda ba za a iya gane shi ba.
Ita ma dai mahaifiyar yaran ta tsallake rijiya da baya daga gobarar da raunuka tare da tagwayenta ‘yan wata 18 wadanda ‘ya’yan mutumin ne.
A lokuta da dama rikici kan kaure a tsakanin ma’aurata wanda a yanayi irin wannan kan tilasta musu danganawa ga kotu domin a raba auren ko kuma a samar da mafita don gyara aure tsakankanin ma’auratan.
A nan gaba ne za a gurfanar da mutumin da ake zargi da danyen hukunci a gaban kotu, bayan ‘yan sanda sun kammala bincike a kan musabbabin yunkurin ƙona yaran da sanadin mutuwar daya daga cikinsu.