Labaran Hausa

Wannan shi ne mutum da yayi shekara 20 batare da yasha Ruwa ba

Wannan shi ne mutum da yayi shekara 20 batare da yasha Ruwa ba

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

Wani mutum mai suna karton Rastafari wanda akewa lakabi da Rastaman dan kasar Burindi, ya bayyana cewar shekarunsa 20 ba tare da ya sha ruwa ba.

Rastaman ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da yan uwansa.

Na daina shan ruwa ne tun shekaru 20 kuma ina gabatar da rayuwata a cikin kwanciyar hankani kamar sauran mutane.” Inji shi

Sai dai Rastaman bai bayyanawa ya uwan nasa dalilinsa na yin hakan ba, ya dai shaida musa cewar ya daina shan ruwan ne ba tare da wani dalili ba.

Hakan ya al’umma cikin mamaki da cece-kuce ganin yadda ruwa yake da matukar amfani ga rayuwa, domin da shi kowane mai rai ke rayuwa, amma shi Rastaman ya bayyana cewar yana gabatar da rayuwansa ne ba tare da ya sha ruwa ba.

A Wani Labarin Na Daban

Yadda Yan Bindiga Suka Mayar Da Kauyukan Zamfara Wajen 50 Kufai
Har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a garuruwa da dama na yankunan kananan hukumomin Gumi da Bukkuyum na Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Yanzu haka fiye da garuruwa 50 na neman zama kufai a yankunan kananan hukumomin sakamakon yadda hare-haren ‘yan bindiga suka tilasta wa jama’ar garuruwan yin gudun hijira zuwa wasu sassan jihar da makwaftan jihohi.

Hakan kuma na aukuwa ne duk da kudaden FCEharaji fiye da naira miliyan dari da ‘yan bindigan suka karba daga hannun mutanen garuruwan, bisa yarjejeniyar ‘yan bindigan za su bari a gudanar da ayyukan noma, a kuma girbe kayan amfanin gona.

Mannir Sani Fura Girke, dan jarida nem ai binciken kwakwaf kan harkokin tsaro, ya shaida wa BBC cewa, na yi yarjejeniya da ‘yan bindigar da kuma garuruwa 55, inda suka yar da cewa ba zasu kara kai hare-hare ba muddin aka biya su kudin haraji

Ya ce,” Dukkan garuruwa 55 din sai da suka biya kudinsu wasu miliyan uku wasu miliyan hudu haka aka tara aka basu naira miliyan 172 da dubu dari biyar.”

Dan jaridar ya ce ana ga kamar abin ya yi sauki za a samu damar aikin gona, sai yanzu suka sake dawo wa suna kai hare-hare.

“ Wadannan hare-hare sun sanya wadannan garuruwa cikin halin ha’ula i, saboda gaba dayan mutanen da ke zaune a garuruwan da ma kauyukansu duk sun yi gudun hijira.”

Mannir Sani Fura Girke, ya ce yawancin kayan amfanin gonar da suka yi suke bukatar a kwashe su duk sun zube a kasa, sannan kuma tun da ‘yan bindigar suka lura cewa mutane sun bar garuruwansu sai suka koma cinnawa kayan amfanin gonar wuta.

Dangane da batun jami’na tsaro kuwa, dan jaridar ya ce a gaskiya duk wadannan garuruwan ba bu jami’na tsaro sai dai a kananan hukumomi suke.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta ce jami’ansu da ma sauran  jami’na tsaro na sane da irin matsalar tsaron da ake fuskanta a garuruwan kananan hukumomin na Gumi da Bukkuyum.

SP Muhammad Shehu, shi nem ai magana da yawun rundunar ‘yan sandan a Zamfarar, ya shaida wa BBC cewa, hadin gwiwar jami’na tsaro na nan na daukar matakan da suka dace a wadanann yankunan don magance matsalar.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button