Kennywood

Shin Da Gaske Ne Anyiwa Hajiya Nafisa Fyade Shine Dalilin Cire Ta Izzar So

Shin Da Gaske Ne Anyiwa Hajiya Nafisa Fyade Shine Dalilin Cire Ta Izzar So

A yan kwanakin nan jita jita ke yawo kan daya daga cikin manyan jaruman Izzar So na anyi mata fyade shine dalilin daina fitowar ta a cikin shirin na Izzar So dalilij wani hoto da bidiyo wanda suke yawo ya saka mutane da yawa sun yarda.

Dukkan alamu sun nuna haryanzu wannan jaruma idonta bai kai kan wannan mummumnar jita jita da take yawo kanta ba. Domin idan idonta yakai zatayi magana saboda tana daya daga cikin jaruman da idan akayi masu sharri suke kokarin kwato yancinsa ta hanyar yin bidiyo ta karyata zargin.

24blog tayi bincike ta gano wannan maganar fyade na Aisha Najamu wato hajiya Nafisa Izzar So ba gaskiya bane babu wanda yayi mata fyade kuma tana cikin koshin lafiya. Tsarin film ne ya fidda ta a ciki amma idan lokacin dawowarta yayi a yadda aka tsara film din zata dawo.

Duk wasu bidiyo da hotuna da ake yadawa a shafukan soshiyal midiya kawai an hada su ne domin a dauki hankalinku ku mutane ku yarda cewa ita aka yiwa fyade domin kuyi ta yadawa kuma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button