Kennywood

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta Kama Wanda ya yaɗa kalaman ɓatanci akan Jarumin Kannywood

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta Kama Wanda ya yaɗa kalaman ɓatanci akan Jarumin Kannywood

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

Rundunar Yan sandan Jihar Kano ta Samu Nasarar kama wani matashi mai Suna Imam Abdullahi indabawa mai Kimanin shekaru 30 a duniya bisa zargin yaɗa kalaman bata suna tare da neman wasu kuɗaɗe daga Abdulaziz Sha’aibu Wanda aka fi sani da Malam Ali na cikin Shirin kwana casa’in tare da yi masa barazanar cigaba da bata masa suna idan bai biya shi wasu kudade ba.

Jarida Radio na ruwaito Hakan na kunshe cikin wata tattaunawa da Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa yayi da wanda ake zargi da mai ƙara a yammacin talatar data gabata, a shedikawatar yan sanda dake Bompai a Kano.

Matashin da ake zargi ya amsa laifin sa a gaban lawyan sa, inda ya nemi da ayi masa afuwa bisa abubuwan da ya aikata na kuskure. Ya kuma bayyana cewa shi mai wa’azi ne da ya samu zamiya yayin wa’azin sa, har ta kai shi ga wallafa rubutun da ya taba mutunci da ƙima ta Jarumin Kannywood Abdulaziz Sha’aibu.

A nasa bangaren, Jarumi Abdulaziz Sha’aibu ya koka matuka da yanda a cewar sa matashin ya cutar da shi da rubutun da ya wallafa, inda ya kara da cewa, Indabawa ya nemi ya bashi kudi don ya dakatar da yaɗuwar wannan rubutu na cin mutunci da take masa, tare da yi masa barazanar cigaba da yada wasu rubuce-rubucen a wasu kafafen muddin bai bashi kudi ba.

Tuni dai rundunar yan sanda sun kammala bincike kuma zasu mika wanda ake tuhuma zuwa kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button