Ni Banga Wani Dalili Da Zaisa Yan Najeriya Suce Suna Fama Da Yunwa Ba Kuje Kuyi Noma Mana ~ Muhammad Buhari

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW
Ni Banga Wani Dalili Da Zaisa Yan Najeriya Suce Suna Fama Da Yunwa Ba Kuje Kuyi Noma Mana ~ Muhammad Buhari
A Hira Da Wani Gudan TV Shugaban Ya Bayyana Haka Ga Bidiyan A Kasa
Sai dai kuma Datti assalafy Ya mayar masa da raddi
ABIN KUKA ABIN TAKAICI
Ashe Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da saninsa ya azabtar damu da yunwa?
Anya kuwa wannan Baba Buharin mu Maigaskiya ne da muka zaba har yake mana gatse da horon yunwar ciki?
Anya kuwa maciya amana basu canza mana shi ba kuwa?
Hakane talaka yaje yayi noma, to ina kudin taki? buhun taki daga dubu 3 ya kuma dubu 23 ta ina talaka zai iya noma ba’a bashi subsidy na taki ba?
Ina talaka zai je yayi noma kidnappers suna sace su? me yasa aka gagara samar da tsaro a inda talaka zaiyi noma? Buhari bai san da wannan ba? wasu guraren sai sun biya kidnappers haraji kafin su bar su suyi noma, ko shekaran jiya a Katsina kidnappers sun sace manoma sama da 30
Da na saurari wanna cikakken hira da akayi da Baba Buhari Maigaskiya sai da na kusan zubar da hawaye saboda takaici da bakin ciki
Dattijo Baba Buhari yana magana kamar bai san abinda yake faruwa ba, kuma wannan duk makircin rahoton karya ne da maciya amana barayi suke kawo masa ya hau kai ya zauna
Har abada ina kaunar Shugaba Buhari, Wallahi maciya sun cuci shugaba Buhari, sun bata masa kyakkawan tarihinsa, kuma wai a hakan suke so ku sake zabarsu saboda ba mu da hankali
Allah Ka isar masa tare da mu gaba daya