Matan arewa

Ku Kalli Yadda Yadda Asirin Wa babbar Hajiya Tatonu

Ku Kalli Yadda Yadda Asirin Wa babbar Hajiya Tatonu

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

Tun farkon tashin rayuwar ta ,zata kasance mai dogon burin rayuwa ta yadda bata hangen kasa da ita,” kullum saman ta take hangowa.

Ga matukar raina duk abinda aka bata,zata ga ko kadan wannan abun ai ba akan tsari yake ba.

Zata fara da tinkahon neman arziki ido a rufe,ba tare da tayi tunanin cewa shi arziki na ubangiji ne.

A lokacin zata fara abinda taga dama.

” A LOKACIN ZATA FARA SAMUN MASU NEMAN AURAN TA”,

duk zata raina masu wayo taga ta wuce ajin su,

tana tnkahon ita “matar manya ce”

duk saurayin dayazo wajanta ko kadan bazata saurare sa ba,karshe ma tace mishi mutunci tana nuna mishi cewa ita fa matar manya ce.

Bakaramin farin jini da tashi takeyi a lokacin ba, saboda takasance kyakkyawar matashiya a lokacin.

Ko kadan zuciyar ta baya kai kan samarin da suke sintiri a wajan ta ba,ita babban burin ta tasamu mai kudi mai hawa babban mota,ta shiga fantamemen gida taganta tana jan mota.

A kullum shine mafarkin

👉 Da yawa akwai su wasu ‘yan matan masu dogon buri a rayuwar su,kuma wannan burin da suke daurawa ran su bawai wani alkhairi bane,buri ne kawai na rashin gaskiya,domin abinda suke irin burin sa wani bashi da wata amfani ga rayuwar su,wasu daga irin wannnan daukan burin karya din suke fadawa hanya halak kuma wasu suke fara karuwan ci,sun lalata rayuwar su kuma.

👉 Irin masu wannan burin sune zaka ga sun saka karya a rayuwar su.

Duk namijin da zaizo wajan su sai suna raina sa suna hangen babban buri,wata tace.

_ bazan auri miji talaka ba sai mai kudi babbban mai kudi,takan mata shi arziki na Allah ne kuma fatan nagari shine gaba da komai.

_ bazata auri namijin da bashi da gida ko mota ba.

_Ba zata auri namijin da ba kyakkywa ba.

_Ba zata kula namijin da ba dan babban gida ba.

_ sai nuna karya koda kowa ita bakomai bace

_irin wadannan matan sai nuna karya alhalin ba komai bane su.

_irin sune masu karyar iyaye ko muhallin iyayen su idan bama su hali bane,sai suna bin gidajen kawayen nasu masu hali suna fadin nan ne gidan su saboda wata karyar manufar su,wanda babu abinda zai kai su sai zuwa hallaka.

👉 A lokacin duk namijin da zai nuna kauna a gare su,indai ba irin wanda suke buri ba to wannna namijin zai fuskanci wulakanci daga gare su,basu da lokacin sa dogon burin su na KWADAYI mabudin wahala shine dai a cikin zuciyar su.

👉 Sai kuma tafiya yayi tafiya sun ga wannan burin nasu fa bai cika ba lokaci kuma ya kure masu sai su fara neman miji ido a rufe.

👉 A lokacin kuma dama ta wuce masu sai a fara nadamar karyar da burin marar amfanin da suka daurawa wa zuciyar su.

👉irin wannnan buri marar amfani ki cire shi daga zuciyar ki.

👉 Kiji tsoron Allah domin idan zuciya tana da tsoron Allah da yawa mutum bazai iya aikata abu marar kyau ba.

👉 Ki sani ita rayuwar mace bata da dogon zango, ki lura ki zama mutuniyar kirki.

👉 Bari kiji in har ke mutuniyar kirki ce kin tsare mutuncin ki kina kula da addinin ki,zaki mamakin nagartattun mazan da zasu nuna kaunar su a gare ki, amma ki sani idan kin watsar da tarbiyyar ki lallai mazan banza ne zasu na biye da rayuwar ki.

👉 Alllah ya shiryar damu akan hanyar gaskiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button