
CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW
Kalli Yadda Asirin Wani Boka Ya Tonu
LIKITA SHIN BAKU DA MAGANIN RAGE SHA’AWA NE, INA DAF DA AFKAWA ZINA, KARFIN SHA’AWATA YAI YAWA
💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐
AƘallah cikin sati guda na sami makamantan wadannan tambayoyin guda takwas, Wanda tambayoyi 6 sun fito ne daga Maza, 2 kuma daga Mata. Amma intattara adadin irinsu zan daga farkon shekara zuwa yau toh wallahi nima bansan adadinsu ba irin wadannan tambayoyin.
Ko shakka babu duk wanda ya dosoka da irin wannan tambayar toh alamace ta mutum yana da tsoron Allah. Yana matukar tsoron Allah, yana kuma tsoron saɓamasa, domin wanda ke bin son zuciya bazai ma taɓa tunanin neman shawara ko mafita ba, abunda kurum zuciyarsa ta basa shi yake yi.
Shyasa yau Matasa da yawa sun kashe gobensu batare da sun san hakan ba, yayin da suka shagala zagin gazawar shugabanni…. sun mance Zina da Talauci tamkar Hanta da Jini ne, basa rabuwa, inde akwai yin kudi a agenda dinka kuma kake aikata zina toh ka dena yaudarar kanka gaskiya… inko kaga me kudi na zina toh ka tausaya masa domin tabbas babu kokonto Arzikinsa na lahira yake cinyewa tun anan don haka sune ubangiji ya kirasu da AL-ASHQA talakawan lahira, zasu shiga wuta ma’abociyar zafi.
Sannan a irin haka wasu illarsu ma sai sun duba Mata masu mutunci, masu addini, sun nuna musu so kuma Matan sun da soyayya sun basu, har tayi tasiri azukatan sisters din… sannan kaga sun fara shigo musu da zantuka da abanen banza…. 😢😢 wai su irin wannan nagartattun suke son ɓatawa koma su ɓata “subahanallah🤦🏻♂️, wanda wannan cin amana ne, hakan na nuna babu wanda ya tsira
Domin mu ba ma’asumai bane, komi addinin Mace wani namiji nada tasirin iya warware tarbiyyarta ta shekara 25 cikin minti 5 wallahi, musamman inta bashi yadda bata ta6a zaton cutarwa daga garesa.
Toh Allah ka cigaba da tsare yan uwanmu damu kanmu daga sharrin sha’awa tare da masu biyemata amin.
🤍 🤍 🤍
Saide dangane da waccan tambayar akoda yaushe bada idon likitanci kurum muke kallon matsala ba, wata matsalar bata bukatar shan kwayoyin magani kurum magana takeso taji na karfafa guiwa daga wanda zuciyar ta nutsu kuma aminta dashi wanda likitoci na ciki, domin matarka na iya boyema damuwa amma intazo gaban likita ba abunda bazata amayar ba saboda waraka take nema.
Allah shi yayewa duk sauran al’umma dake fuskantar hakan, domin na tabbata irin wannan larurar ta tsananin sha’awa kwai tarin mutane cikin Maza da Mata masu fama, bakowa bane mazinaci duk da lalacewar zamani.
Amma anan inason tunasar damu irin girman laifin zina, ita ZINA sam bata kashe sha’awa, tana kasheta ne kurum na ɗan wani lokaci wanda daga sanda aka farata tohfa mutum ya budewa kansa kofar talauci, kaskanci, kuncin rayuwa, nadama, lalacewar jiki, asara da masifu gakai.
Kai uwa uba ma mahaifanka ko mahaifanki ba irin ɗa ko ƴar da sukai fatan ace sun haifa ba kenan, sun raineka ne ka zama mutumin kwarai, ko mutuniyar kwarai domin duk abunda kayi koda bayan ransu suna da kamashon aikin dakai kuma zaije musu a kabari.
Duk shari’oin Allah ba wanda ZINA ba ta rusasu, cikakkiyar fitsara ce, cikinta ake samun dukkan wani nau’in sabon Allah, raunin addini, raunin aqidah, rashin kishi, rashin ganin girman manzon Allah, kisan kai, annamimanci, karya, cin amana, tare da bude kofofin talauci da annoba ga hatta wanda baiji ba, bai gani ba.
Duk tsananin sha’awarka akwai wanda suka fika, domin wasu hadda larura kuma hakan baisa sun biye mata sun saɓawa Allah ba. Kai ko mahaukacin dake yawo a bola yana da sha’awa amma bai zina da mahaukaciya yar uwarsa ba ballantana kai mai hankali da tunani.
Muddin ka kuskura ka fara zina tohfa ko kai aure ba baki naiwa mutum ba amma da wuya ya dena, domin maganinta shine kar afara.
🤎 🤎 🤎
■- Shawara ta farko anan ga duk wanda ke cikin yanayin wallahi muddin yana da halin aure toh kai tsaye yai AURE koda hakan na nufin tsayawar karatunsa muddin bazai iya riqe kansa ba. Yafi kaje kana jawowa mahaifa da ýan uwa abin kunya tare da karin masifu akan mu sauran al’umma wanda dama ayau gasu muna ciki na kashe-kashe da sace-sace da annoba, duk zina na daga sillar haka.
Don haka tunda mutum gashi ya balaga jikinsa ya nuna yanason auren toh ya nemi tallafin iyayensa inma baida halin yi, ko tallafin yan uwansa ya sanar dasu bukatarsa ta aure afili su tallafa, babu sama dasu.
In kuma ba halin abun auren to ka nemi ataimaka ma da jarin sana’ar yi wacce in Allah ya dubi niyya sai kaga yasa albarka ciki ka sami abunyin auren.
Musulunci addini ne da aka ginashi don acire barna cikin jama’a akawo musu gyara. Yau da gobe tabbas itace aure, inza’ai dole ya zamto akwai abun iya rike iyalin. Amma de aure misamman ga namiji baya hana karatu sam-sam, saide kurum tunanin karin nauyi, amma in haka ta faru biyun sun taso lokaci guda toh azaɓi mafi mahimmanci abar daya, wanda anan auren yafi mahimmanci.
Ko bangaren iyaye rashin fahimtar addini ne kace yaro ko yarinya sai yayi karatu dole kafin ai masa aure alhalin ya baytana yana da bukata, inbai bayyana ba shikenan, tunda da akwai masu iya jurewa har su kammala karatun lami lafiya amma basu da yawa. Don haka da wannan qin karatun ai aure da kuma yaro yaje ya kama zina wanne yafi muni? Zina tafi ILLAH.