Labaran Hausa

Innalillahi Yadda Wata Budurwa Ta Mutu A Dakin Saurayin Ta

Innalillahi Yadda Wata Budurwa Ta Mutu A Dakin Saurayin Ta

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

A yau muke samun wani mummunan labarin wata budurwa wacce ta mutu a dakin saurayin ta. Wacce ta kasance ita daliba ce karatu taje tana a matakin jami’a wato (Degree). Wannan budurwa tana karanta lissafi ne tana a aji ukku wato (Level 300).

Ta ziyarci saurayin nata ne tare da kawarta itama kawarta ta kasance daliba ce amma ba makaranta daya suke ba. Kamar yadda rahoto ya nuna lokacin da wannan budurwa taje wajen saurayin nata ya dafa masu shinkafa ne. Amma a daidai lokacin da budurwa take tsakiya da cin abincin sai ta kama ciwon ciki.

Ba jimawa take anan tace ga garin ku ma’ana ta mutu duk da saurayin nata da kawarta sunyi kokarin ceto rayuwar ta. Wani makwabcin gidan saurayin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Rundunar yan sanda sun tabbatar da za’ayi bincike kan lamarin. Kawarta da saurayin nata yanzu haka suna daure a kurkuku. Yan sandan kuma sun bayyana lokacin da aka kira su dauki gawar sun dauke ta ne sun kaita gidan ajiyar gawarwaki.

Allah ya kyauta. Kuma ya kiyaye ameen.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button