Labaran Hausa

Innalillahi Ku Kalli Yadda Aka Kama Yara Kananu Suna Iskanci A Cikin Makaranta

Innalillahi Ku Kalli Yadda Aka Kama Yara Kananu Suna Iskanci A Cikin Makaranta

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

TA’ALIƘI AKAN AMFANIN AUREN MACE MALAMA

“Ni na san amfanin auren mace mai ilimi” cewar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahul-Lah) a cikin wani jawabi taƙaitacce da malamin namu ya yi a firar sa da Freedom Radio.

Ba shakka wannan jawabin na malam haka yake. Mun gwada mun ga alfanun hakan a aikace. Mace mai ilimin addini in dai aka dace tana aiki da ilimin, ba ta zama cikin tawagar su Bil Amu Ɗan Ba’urah ba, to gaskiya duniya ce, kamar yadda ya zo a hadisin Muslim cewa: “Duniya wurin jin daɗi ne, kuma abu mafi alheri a duniyar shine mace ta gari”.

Daga cikin alfanun hakan shine in kana da mace malama mahaddaciya mai aiki da ilimin ta za sami natsuwa game da makomar yaran ka. Haka za ta yi ta kimsa musu karatu a ɗaka, kafin ka ankara sai ka ji sun haɗa hadda, sun sauke littafai dabam dabam.

Wani abin sha’awa ma shine, ni dai ina iya wuni a gida ban kula malama ba, in dai wayoyina da change ga laptop ɗita da kuma ruwan shayi lafiyayye zan iya wuni ban kula kowa ba, ita kuma ta yi ta tilawar ta, ko ka jiyo ta a can cikin gida tana karɓan hadda a wajen ɗaliban ta. Ka san in ka auri jahila za ta iya wafce littafin ka ta wurgar sannan ta ce maka wai kai ba ka da aiki ne sai karatu kamar alhudahuda?

Daga cikin abin da na tsana akwai assignment. Ka san malaman islamiyya da shegen son-a-sani; wai gaishe da uwar saurayi a kasuwa. Ana zaune lafiya, sai su je su ba yara wani assignment mai wahala. To in matar ka malama ce ba ruwan ka, duk yaron da ya ce Abba an ba mu aiki sai ka ce masa je ka gun maman ku.

Wani abin ban sha’awa da mace malama shine, galibin su suna da haƙuri da juriya da mai da komai ga Allah. In ka yi ma ta laifi ko in kana da wani annoying habit irin namu na maza ko kuma a halin ƙuncin rayuwa sai ta dinga tuna rayuwar sahabbai da irin juriyarsu. Haka kuma ka ga ita mace malama ba ta cika damuwa da yawan zuwa biki ko suna ba.

Matsalar mace malama dai kawai ita ce ba kasafai za ka iya samun halin yi mata wayau ko ka kawo mata waƙar larabci ka ce mata nafsi ne ba.

Baya ga wannan kuma in ka auri malama, musamman, in tana koyarwa a Islamiyya, to da wuya ka iya ƙara aure; saboda malama akwai ta da iya kashe wa miji kasuwa; to duk ƴan matan auguwa ɗalibanta ne, in ma ka je wani gari ko wata anguwa ka fara nema, da an ce ai matarsa malama ce shi kenan, an maka own goal.

Shi ya sa yake da kyau iyaye su dage wajen ganin ƴaƴansu mata sun sami ilimin addini mai nagarta.

PLS HIDE MY ID

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button