Labaran Hausa

Gwajin gawa ya bayyana dalilin rasuwar ɗan Davido

Gwajin gawa ya bayyana dalilin rasuwar ɗan Davido

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

Jaridar Punch ta rawaito jami’in hulda da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar.qq

Hundeyin ya ce, “An kammala gwajin gawar kuma sakamakon ya tabbatar da cewa yaron (Ifeanyi) ya nutse wa ya yi a ruwa.”

Tun a baya a ka bayyana cewa akwai yiwuwar ƴan sanda su gudanar da bincike don gano ko Ifeanyi ya mutu ne sakamakon nutsewa a cikin wani ruwa da ke gidan mahaifinsa da ke unguwar Banana Island a jihar Legas.

Wata majiya mai tushe wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce yana cikin ɓangaren ayyukan ƴan sanda su gudanar da binciken gawa a irin wannan yanayi, ta kuma kara da cewa idan iyalan mamaci ba su amince da yin gwajin ba to sai ƴan sandan su hakura.

Mahaifiyar mataimakin ɗan takarar gwamna na NNPP a Kano ta rasu

Hajiya Rabi Abdullahi, mahaifiyar mataimakin ɗan takarar gwamna na NNPP a jihar Kano, Comrade Aminu Abdulsalam ta rasu.

Ɗan takarar gwamna na NNPP a jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da rasuwar a wani gajeren sako da ya yaɗa ta kafar WhatsApp a yau Asabar.

Sanarwar ta Abba Gida-gida ta ce za ayi jana’izar marigayiyar a masallacin Alfurqan da ke titin Alu Avenue a cikin birnin Kano da misalin ƙarfe 4 na yamma.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button