Labaran Hausa

Dubun wata ƴar aiki ta cika, yayin da aka kamata tana kokarin sanya maganin kwari a ruwan shan uwargidanta Innalilahi

Dubun wata ƴar aiki ta cika, yayin da aka kamata tana kokarin sanya maganin kwari a ruwan shan uwargidanta Innalilahi

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

Dubun wata ƴar aiki ta cika, yayin da aka kamata tana kokarin sanya maganin kwari a ruwan shan uwargidanta.

A wani bidiyo da nan da nan ya karade shafukan sada zumunta, an ga ƴar aikin ta durkusa kan guiwoyinta tana amsa tambayoyin uwargidan na ta bayan an yi ram da ita. Kamar yadda labarin yazo daga shafin internet na Fikira24.

Ta bayyana dalilan aikata hakan

Ƴar aikin gidan ta bayyana cewa tayi alkawarin sai ta halaka duk wanda ya gaya mata wata maganar da ba tayi mata dadi ba a rai.

A cewar ta, ta cire ƴan makullan dakin matar gidan daga wurin da aka saba ajiye su, ta shiga dakin sannan ta sanya gubar a cikin ruwan shan ta.

Sai dai tayi rashin sa’a domin duk wannan tuggun da take shiryawa an dauka a kyamara yayin da take aikatawa.

Ba a san takamaimai dalilin da yasa take kokarin halaka matar gidan ba. Wannan lamarin dai ya sanya mutane da dama tunanin ko wane irin abu matar gidan take yiwa ƴar aikin da har ya sanya tayi tunanin ta cutar da ita, yayin da wasu kuma sun goyi bayan matar gidan inda suka bukace ta da ta gaggauta korarta daga gidan.

Azabtar da ƴar aiki

Sau da dama ana zargin yadda wasu ke azabtar da aikin, wanda ake ganin hakan yana wuce kima kwarai da gaske, to sai dai wasu na da ra’ayin cewa hakan ba wani abu bane.

Wasu daga cikin ƴan Najeriya na goyon bayan matar gidan inda suka bata shawarar da ta koreta daga gidan ba tare da bata lokaci ba.

Kunji abun da yafaru wannan shine dan haka ya kama ta jama’a kuyi hattara wanda suke da masu yan aiki su dai na wahalar dasu domin kada su kashe su, aure maza jansu.

To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button