Labaran Hausa

Bidiyon Yadda Wani Saurayi yake taɓa ñonon Budurwa sa a gidan gala

Bidiyon Yadda Wani Saurayi yake taɓa ñonon Budurwa sa a gidan gala

Bidiyon Yadda Wani Saurayi yake taɓa ñonon Budurwa sa a gidan gala

Bidiyon Yadda Wani Saurayi yake taɓa ñonon Budurwa sa a gidan gala
Don’t be a LAZY YOUTH abeg, read…😀👇

Kullum in muna waya da shi nakan ce Ummaru ya shirye shiryen bikin? Dafatan ka fara hada lefe ko? Abubuwan da suka rage din suna da yawa ne ko saura kadan? Ya kamata fa ka fara shiri tin yanzu fa dss…

Kullum amsar sa daya shine haba ai shiri yanzu haka ya yi nisa, kusan ma na kammala. Don yanzu haka ina da kadara wacce takai 700k (Dubu dari bakwai) bla bla bla….

Ashe Ummaru kam duk bula ce, babu abinda ya siya sai set na kayan kwalliya 🙄

Har ana sauran 3 weeks biki lefe ko kwata bai hadu ba. Hakanan Yan’uwa mai gyele, mai bag mai shoe, mai atamfa da lace aka lallaba aka hada mai, babban Yayansu kuma ya siya mai akwatunan lefe ya biya mai kudin nagani ina so/saka rana 50.

Ana sauran 3 days daurin aure kawai sai ya bullo da zancen ai baida kudin sadaki wanda shima 50k yake son kaiwa, still so yake nan ma a biya masa.

Bafa don baida sana’a bane, yana da sana’ar sa, kuma yana samun rufin asiri a sana’ar tasa daidai gwargwado Alhamdulillah. Kawai shi wai a hakan yana da wayo ne da gadarar ai yana da Yan’uwa dole dai su masa, tinda in basu yi ba a yanda suke da rufin asiri za su zama abin zargi ne a idon mutane kuma ace sun kasa taimakon sa tinda iyayen sa basa raye duka biyun…. 🙂

Ana nan sai aka yi shawarar a kyale shi har ranar daurin auren a ga gudun ruwan sa. Aiko ana zuwa wajen daurin aure aka ce ina Goron daurin auren Ummaru?

Budan bakin sa wai daman ango ne ke siyan goron da sweet din? Ai shi yama manta da wannan kuma baida kudin siyowa.

Takaici ya kama duk Yan’uwa dake wajen aka fara maganganu.

To sai aka ce shikenan tinda babu wannan kawo sadakin, a daura a hakan.

Ummaru ba sai ya fara zazzare ido wai baida kudin sadaki ba bla bla bla….😕😕😕

Take aka hau zagin sa a wajen kamar su kai masa duka. Abin takaici ga dangin matar a gefe na jira…

Anan sai wani Uncle nasa yace kawai a daura auren a matsayin bashi, bayan an daura ko zuwa gobe ne shi zai kawo kudin sadakin ya bada (Mai kudi ne sosai fa Uncle din nasa, shine Baban Yaya gurin mahaifin angon, kawai ya ki badawa ne don ya koya masa hankali a cewar sa bayan daura auren)

Habawa! Ai sai Ummaru ya daka tsalle ya fara hawaye yace wallahi shi ba wanda zai daura masa a bashi, ai wannan abin kunya za su ja masa kaza kaza kaza… 😐

Kawai yace a jira sa yana zuwa. Bayan wasu yan mintuna sai gashi ya dawo da 50k (dubu hamsin) a hannun sa, wai bashi ya samo a wajen wani abokin sa, amma abokin yace gobe yake bukata ya maida masa kudinsa (Saboda ya ji Uncle nasa a baya yace zai bada 50k din washegarin daurin auren) anan aka gane yana da kudin sadakin iskanci ne kawai da son na banza irin nasa.

Haka dai aka daura aure ran kowa bace a wajen. Ana gamawa kuwa suka shiga da shi dakin zaure suka masa tatas kamar su zane shi. Shiko kai na kasa sai hakuri yake badawa.

In takaice muku labari bayan daurin auren ango ya shigo cikin gida sai aka ce Ummaru ga abubuwan da Yan’uwa wasu suka zo maka da shi a matsayin gudumawa sai ka musu godiya.

Budar bakin sa sai cewa ya yi “Mutum in don Allah ya yi min miye zai jira na zo nace masa na gode😒” 😄😄😄

Suka budi baki kawai suna kallon sa da mamakin karfin halin sa… 😀

Meyasa na baku labarin abinda ya faru?

Na baku labarin nan ne saboda nasan yanzu haka akwai masu tinani irin na Ummaru cewa ai suna da Uncle mai kudi ko Aunty mai kudi don haka in lokacin biki ya zo dole su zasu masa komai.

Ya Dan’uwa ka daina sakankancewa da yawa, rayuwa ta yi tsada yanzu, kowa aka barshi da bukatun sa kadai ma sun ishe shi. Zaka iya samun gudumawar Yan’uwa da abokai, Amma ka sani ko iyaye yanzu daddaya ne suke dauke ma ‘Dansu lefe, su ake cewa an ma auren gata, a samo musu mata a yaran abokai kuma a dauke musu hidimar biki… (Yaran masu dollars kenan) 🙂

Kar ka ji haushin kowa in bai taimaka maka lokacin hidimar biki ba, kai dai in ka san ka shirya ma aure to ka fara tanadi tin da wuri. Suma Yan’uwan in sun ga ka yi nisa a tara kayan sun fi jin karfin gwuiwar taimakawa gaskiya.

Akwai sana’oi a Arewa kala kala da zasu baka daman tara kudi a hankali sai dai girman kai ya hana ka gwadawa. A kula dan Allah, kar a zo ana danasani! 🙂

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button