Labaran Hausa

Bello Turji yayi magana akan matashin da yace yana son Matar sa kalli video

Bello Turji yayi magana akan matashin da yace yana son Matar sa kalli video

CLICK HERE TO WATCH FULL VIDEO NOW

Bello Turji yayi magana akan matashin da yace yana son Matar sa kalli video
Shahararran dan ta’adda Bello Turji ya bayyan cewa, a shirye yake ya nuna wa gwamnati wasu mayanka da ake yanka ’yan uwansa a yankin da yake.

A hirar da Bello Turji ya yi da Aminiya a maboyar sa wanda ya fitini jihohin Zamfara da Sokoto yace, akwai mahauta akalla guda biyu da aka ware domin yanka ’yan uwansa amma gwamnati ba ta sani ba.

Sannan Bello Turji ya yi ikirarin cewa, tausayin talakawa da jami’an tsaro suke kashewa ne yasa shi rubuta wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasikar neman zaman lafiya.

Kafin Mu Ci Gaba Ga Kadan Daga Cikin Rohotonnin Rashin Tsaro A Zafara

Har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a garuruwa da dama na yankunan kananan hukumomin Gumi da Bukkuyum na Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Yanzu haka fiye da garuruwa 50 na neman zama kufai a yankunan kananan hukumomin sakamakon yadda hare-haren ‘yan bindiga suka tilasta wa jama’ar garuruwan yin gudun hijira zuwa wasu sassan jihar da makwaftan jihohi.

Hakan kuma na aukuwa ne duk da kudaden FCEharaji fiye da naira miliyan dari da ‘yan bindigan suka karba daga hannun mutanen garuruwan, bisa yarjejeniyar ‘yan bindigan za su bari a gudanar da ayyukan noma, a kuma girbe kayan amfanin gona.

Mannir Sani Fura Girke, dan jarida nem ai binciken kwakwaf kan harkokin tsaro, ya shaida wa BBC cewa, na yi yarjejeniya da ‘yan bindigar da kuma garuruwa 55, inda suka yar da cewa ba zasu kara kai hare-hare ba muddin aka biya su kudin haraji

Ya ce,” Dukkan garuruwa 55 din sai da suka biya kudinsu wasu miliyan uku wasu miliyan hudu haka aka tara aka basu naira miliyan 172 da dubu dari biyar.”

Dan jaridar ya ce ana ga kamar abin ya yi sauki za a samu damar aikin gona, sai yanzu suka sake dawo wa suna kai hare-hare.

“ Wadannan hare-hare sun sanya wadannan garuruwa cikin halin ha’ula i, saboda gaba dayan mutanen da ke zaune a garuruwan da ma kauyukansu duk sun yi gudun hijira.”

Mannir Sani Fura Girke, ya ce yawancin kayan amfanin gonar da suka yi suke bukatar a kwashe su duk sun zube a kasa, sannan kuma tun da ‘yan bindigar suka lura cewa mutane sun bar garuruwansu sai suka koma cinnawa kayan amfanin gonar wuta.

Dangane da batun jami’na tsaro kuwa, dan jaridar ya ce a gaskiya duk wadannan garuruwan ba bu jami’na tsaro sai dai a kananan hukumomi suke.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta ce jami’ansu da ma sauran  jami’na tsaro na sane da irin matsalar tsaron da ake fuskanta a garuruwan kananan hukumomin na Gumi da Bukkuyum.

SP Muhammad Shehu, shi nem ai magana da yawun rundunar ‘yan sandan a Zamfarar, ya shaida wa BBC cewa, hadin gwiwar jami’na tsaro na nan na daukar matakan da suka dace a wadanann yankunan don magance matsalar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button